An kashe 'yan ta'adda 50 a wasu farmakai da jami'an tsaron Mozambik suka kai a cikin kwanaki 2 a arewacin kasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida Amade Miquidade ya shaida cewar a cikin kwanaki 2 an kai wa 'yan ta'adda farmakai a kan hanyar Chinda-Mbau ta jihar Cabo Delgado da yankin Quissanga.
Miquidade ya ce a ranar Alhamis din nan a kan hanyar Chinda-Mbau ankashe 'yan ta'adda 42 inda a ranar Juma'ar nan a yankin Quissanga kuma aka kashe wasu 8.
Tun shekarar da ta gabata zuwa yau ake kai hare-haren ta'addanci kan gine-ginen gwamnati da jami'an tsaro a Mozambik.
Ana dora alhakin kan wata kungiya da ake kira Al-Shabab amma har yanzu ba a sani ba ko tana da alaka da ta Somaliya.