A dauki ba dadin da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan ta'dda akan iyakan Burkina Faso a kasar Mali an kashe 'yan ta'adda 15.
Kamar yadda kafafen yada labaran cikin gida suka sanar sojojin Faransa sun kaddamar da farmaki akan wasu 'yan ta'adda dake da alaka da Alka'ida a yankin Boulikessi dake kasar Mali a ranar 9 ga watan Janairu.
A harin an magance 'yan ta'adda 15 tare da kwace makamansu da dama.
A harin Barkhane da sojojin Faransa suka fara a Mali daga watan Disamba kawo yanzu sojoji 5 sun rasa rayukansu.
A kasashen Nijer, Cahd, Burkina Faso da Mali a farmakin Barkhane da aka fara a shekarar 2013 kawo yanzu da sojoji dubu 5 da 100 an samu hasarar rayukan sojoji 50.