'Yan sanda 11 ne suka rasa rayukansu, wasu 4 kuma suka bata sakamakon harin ta'addanci da aka kaiwa jami'an tsaro a Burkina Faso.
Kakakin Gwamnatin Burkina Faso Ousseni Tamboura ya fitar da rubutacciyar sanarwa cewa, an kai harin a yammacin Talatar nan a yankin Bilbalogo a lokacin da motar jami'an tsaro ta ke sintiri wasu da ba a san ko su waye ba suka bude mata wuta.
'Yan sanda 11 ne suka rasa rayukansu, wasu 4 kuma suka bata sakamakon harin.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.