Akalla fararen hula 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai a wasu kauyukan Jamhuriyar Nijar da ke iyakar Mali.
Labaran da jaridun Nijar suka fitar na cewa wasu mutane a kan babura ne suka kai hari a kauyuka 3 da ke yankin Tillaberi da ake iyakar kasar da Mali. An kashe akalla fararen hula 20 a lamarin.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin da ya afku a yankin da mafi yawancinsa yake karkashin kungiyar Alka'da a Magrib. Tun shekarar 2017 ake kai wa sojoji da fararen hula hare-haren ta'addanci a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar.
Ana zargin 'yan tawayen arewacin Mali ne suka kai harin.
Tun shekarar 2017 aka aiyana dokar ta baci a yankin Tillaberi da keiyaka da kasashen Mali, Benin da Burkina Faso.