Majalisar dokokin Masar ta sake kara wa'adin dokar ta baci da aka fara kaddamarwa shekaru 4 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labarai na Masar ya shaida cewa, a karo na 17 ana kara wa'adin dokar ta bacin inda daga ranar 24 ga Yuli za ta fara sabon wa'adi na watanni 3.
A watan Afrilun 2017 ne aka kai harin ta'addanci a garuruwan Iskandariyya da Tanta da ke Masar tare da kashe mutane 45 tare da jikkata wasu 125. Kungiyar ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin kai harin.
Bayan hare-haren ne Shugaban Kasar Masar Abdulfatah Al-Sisi ya saka dokar ta baci na tsawon watanni 3.