An kara wa'adin dokar ta baci a Masar

An kara wa'adin dokar ta baci a Masar

Majalisar dokokin Masar ta amince da kara wa'adin dokar ta baci na tsawon watanni 3 a fadin kasar.

Shugaban Majalisar Dokokin Hanafi Jibali ya ce, kaso 2 cikin 3 na 'yan majalisar dokokin sun amince da bukatar Shugaban Masar Abdulfatah Al-Sisi na kara wa'adin dokar ta baci a kasar.

An bayyana cewar dokarta bacin da aka kara har sau 15, za ta fara aiki daga 24 ga watan Janairu 2021.

Bayan harin da 'yan ta'addar Daesh suka kai a garuruwan Iskandariyya da Tante a watan Afrilun shekarar 2017 tare da kashe mutane 45 da jikkata wasu 125 ne aka saka dokar ta baci a Masar.

 


News Source:   ()