Tun a watan Afrilun 2023 ne yaki ya barke tsakanin sojojin Sudan a karkashin jagorancin Abdel Fattah Al-Burhan da kuma dakarun daukin gaggawa na RSF, karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo.
Mummunan rikicin ya tilastawa mutum daya cikin biyar barin gidajensu, yayin da dubun dubatar wasu kuma suka mutu.
Fiye da mutum miliyan 25 a Sudan din wato kusan fiye da rabin al’umar kasar na fuskantar matsananciyar yunwa a yanzu haka wadda ke bukatar dauki cikin gaggawa.
A ranar 14 ga watan Agusta ne Amurka ta bude tattaunawa a kasar Switzerland da nufin rage wahalhalun da mutane ke fuskanta da kuma cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Yayin da tawagar RSF ta bayyana, sojojin Sudan (SAF) ba su ji dadin tsarin ba kuma ba su halarci taron ba, ko da yake suna tattaunawa ta wayar tarho da masu shiga tsakani.
Kasashen Saudiyya da Switzerland ne suka dauki nauyin taron, inda kungiyar Tarayyar Afirka, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya suka kammala duk wani tsare-tsare na samar da wani rukuni na shiga tsakani da zasu taimaka wajen samar da zaman lafiya, abin da ake kira Aligned for Advancing Life Saving and Peace in Sudan Group (ALPS).
"Kungiyar ALPS ta samu shalewa daga bangarorin biyu da ke rikici da juan don samar da isar da kayayyakin agajin jin kai cikin aminci da kwanciyar hankali ta hanyoyi guda biyu wato mashigar yammacin Darfur a Adre da hanyar Dabbah tare da shiga arewa da yamma daga tasahr ruwan kasar Port Sudan," a cewar sanarwar.
Yanzu haka dai Motocin agaji na tafiya zuwa sansanin gudun hijira na Zamzam a Darfur, inda aka ayyana a matsayin inda ke fama da matsananciyar yunwa.
"Wadannan hanyoyin dole ne su kasance a bude kuma a kiyaye su domin mu iya kai agaji zuwa yankin Darfur mu fara kawar da yunwa. Ba za a iya amfani da abinci ko yunwa a matsayin makamin yaki ba,” in ji kungiyar.
Masu shiga tsakani sun ce suna kuma samun ci gaba wajen bude hanyar shiga ta mahadar Sennar da ke kudu maso gabashin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI