A kasar Nijar an kame Sani Saley Guruz wanda ya shirya yunkurin juyin mulkin ranar 31 ga watan Maris.
Kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito an cafke wanda ya shirya yunkurin juyin mulkin kasar Nijar Guruz a ķasar Benin inda aka mika shi a hannun jami'an tsaron kasar Nijar.
A ranar 31 ga watan Maris an ji karar harbe harben bindiga a kusa da fadar shugaban kasa inda aka bayyana lamarin a matsayin yunkurin kifar da gwamnatin kasar.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Zakaria Abdurrahman ya tabbatar da yunkurin juyin mulkin amma ba'a yi nasara ba.
Game da yunkurin juyin mulkin an kame fiye da mutum 15.