An kama jami'an gwamnatin Itopiya 5 bsa zargin su da hannu a kisan gillar fararen hula da yawa da wasu 'yan bindiga suka yi a wani kauye da ke jihar Benishangul Gumuz a yammacin kasar.
Sanarwar da Ofishin Yada labarai na jihar ya fitar ta ce, mutanen 5 daaka kama da ake zargi suna da hannu a ta'annatin, ma'aikatan gwamnatin Tarayya da ta jiha ne.
An kwashe gwamman mutane a harin da 'yan binciga suka kai a wani kauye da ke jihar Benishangul Gumuz in kasar Itopiya.
Wasu majiyoyin sun bayyana cewar sama da mutane 90 sun mutu.
A lokacin da Firaminista Abiy Ahmed ya ziyarci garin Mekele ya yi alkawarin kawo karshen rikicin kabilanci a yankin.