An kama daya daga shugabannin Al-Shabab a Somaliya

An kama daya daga shugabannin Al-Shabab a Somaliya

A Somaliya an kama daya daga cikin shugabannin kungiyar ta'adda ta Al-Shabab.

Kakakin gwamnatin Somaliya Muhammad Ibrahim ya shaida cewa, dakarun soji da 'yan sanda na Somaliya da ke kai farmakan hadin gwiwa a War Isse da Aqab Duco da ke yankin Middle Shabelle sun kama daya daga cikin jagororin Al-Shabab.

A gefe guda, Tashar Talabijin ta Kasa ta Somaliya ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu an kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 130 a hare-haren da ake kai wa a yankin.

A farmakai na karshe da dakarun Somaliya suka kai sun kubutar da kauyuka 6 daga hannun 'Yan ta'addar Al-Shabab.

Dakarun sojin Somaliya sun sanar da mutuwar 'yan ta'addar Al-Shabab 60 a ranar Larabar nan a wani gida da suke zaune bayan fashewar bama-baman da suke hadawa.


News Source:   ()