Dakarun tsaron teku na Libiya sun kama 'yan gudun hijira kusan dubu daya a awanni 48 da suka gabata a lokacin da su ke yunkurin Tafiya Turai ta Tsakiyar Tekun Bahar Rum.
Ofishin Hukumar Yaki da Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, sun mayar da 'yan gudun hijira da suka hada da maza da mata zuwa Libiya.
An bayyana cewa, an kai 'yan gudun hijirar zuwa cibiyar tsare bakin haure da ke kasar.