A Libiya an kama 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba da suka fito daga kasashe daban-daban.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Libiya ta fitar ta ce, jami'an tsaron teku ne suka kai farmaki kan wani wajen ajje kayayyaki da ke garin Zliten na gabar tekun Bahar Rum.
Sanarwar ta ce a lokacin da aka kama 'yan gudun hijirar, sun gama shiryawa don shiga jirgin ruwa a garin Zliten don kama hanyar tafiyar Turai.
An kai 'yan gudun hijirar da aka kama zuwa wajen killace mutane da ke Ofishin Hukumar Kula da Shige da Fice ta yankin.