An kama 'yan bindiga 55 a yayin farmakin da aka kai musu a jihar Ebonyi da ke kudu maso-gabashin Najeriya.
Wani jami'in sojin Najeriya Birgediya Janar Taoreen Lagbaja ya shaida cewa, sakamakon yadda ake samun yawan kai hare-hare a jihar ne ya sanya aka kai wa 'yan bindigar farmaki.
Ya ce, an kama 'yan bindiga 55 a yayin farmakin, an kuma kwace makamai da yawa daga hannunsu.
Lagbaja ya kara da cewa, za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu.
A yammacin ranar 29 ga Maris an kashe mutane 27 a hare-hare 4 daban-daban da aka kai a jihar ta Ebonyi.