Tsohon Shugaban hukumar leken asirin kasar Akol Koor na tsare ne a gidan sa tun bayan da aka dakatar da shi a watan Oktoba, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito, amma ya kasance mai karfin fada aji bayan tafiyar da hukumar tsaron kasar tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 2011.
Dakarun kasar Sudan ta kudu © AFPWata majiyar soji da ake kyautata zaton tana da hannu a harin ta shaidawa jaridar Sudan Post cewa an kama Koor ne bayan kazamin fada da aka ce ya yi sanadin mutuwar sojojinsa da dama ko kuma suka jikkata.
A cikin faɗakarwa ga ma'aikatanta da ke ƙasa, Majalisar Dinkin Duniya ta ba da rahoton harbin da ke da alaƙa da tsare tsohon shugaban hukumar leken asirin, yana ba mutane shawarar su fake. Amma duk da haka babu tabbas ko a zahiri an kama Koor. Da yake tabbatar da harbe-harbe, mai magana da yawun rundunar Lul Ruai Koang, ya ce lamarin ya hada da "jami'an tsaron mu da aka tura wurin domin samar da karin tsaro". "Ba mu san abin da ya faru ba, kuma wannan rashin fahimtar ya tabarbare a cikin harbin bindiga," in ji Koang, ya kara da cewa an harbe wasu ma'aikata biyu tare da raunata kafin a shawo kan lamarin. Hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta da kafafen yada labarai na kasar sun nuna yadda cunkoson jama'a suka tsaya cak a kusa da gidan tsohon jami'in leken asirin, inda direbobin suka yi watsi da motocinsu sakamakon harbin da aka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI