An kaiwa sojojin Faransa harin bam a Mali

An kaiwa sojojin Faransa harin bam a Mali

An jikkata sojoji da dama sakamakon harin bam a mota da aka kai wa sojojin Faransa da ke Mali.

Labaran da kafafan yada labarai na Mali suka fitar na cewa, motar da ke dauke da bam ta nufi sojojin Faransa da ke yankin Timbuktu wadanda suke aiyuka karkashin Farmakan Berkhane.

An jikkata sojoji da dama yayin da aka aike da jiragen sama masu saukar ungulu zuwa yankin.

A ranar 10 ga Yuni Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana za su janye sojojinsu daga Mali wadanda ke kai Farmakan Berkhane.

A farkon shekarar 2013 Faransa ta kaddamar da Farmakan "Serval" a Mali inda a ranar 1 ga Agustan 2014 kuma ta fara kai "Farmakan Berkhane" a kasar.

A kowacce rana ana kashe Yuro miliyan 1 ga Farmakan Berkhane, kuma akwai sojojin Faransa sama da dubu 5 da ke aiyuka a Mali.

 


News Source:   ()