Sojoji 10 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam na kunar bakin wake da aka kai sansanin bayar da horo na sojojin Somaliya.
Jami'in dan sanda Abdifatah Hasan ya shaida cewa, an kai hari na kunar bakin wake a sansanin soji na General Dhabadan da ke yankin Wadajir na Mogadishu Babban Birnin Kasar.
Labaran da kafafan yada labarai na kasar suka fitar sun bayyana cewa, wani mutum 1 da ke tsakiyar sojojin da ke samun horon ne ya tayar da bam din da ke jikinsa inda a kalla mutane 10 suka mutu yayinda wasu da dama kuma suka samu raunuka.
An dora alhakin kai harin kan kungiyar ta'adda ta Al-Shabab.