An kai hari ta sama kan wata kasuwa a Itopiya

An kai hari ta sama kan wata kasuwa a Itopiya

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon hari ta sama da aka kai a kan wata kasuwa da ke yankin Tigray na arewacin Itopiya.

An bayyana cewa, jami'an tsaron Itopiya sun hana ma'aikatan lafiya zuwa wajen da aka kai harin a yankin Togoga na Tigray.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, mutane da dama sun mutu, an kuma kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Gwamnatin Somaliya ba ta ce komai ba game da harin.

 


News Source:   ()