An kafa sabuwar gwamnati a Jamhuriyar Nijar

An kafa sabuwar gwamnati a Jamhuriyar Nijar

Sabon Firaministan Jamhuriyar Nijar Ouhoumoudou Mahamadou ya kafa sabuwar gwamnati.

A ranar 3 ga Afrilu ne Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum ya nada Ouhoumoudou Mahamadou a matsayin Firaministan, kuma ya ba shi umarnin kafa gwamnati mai Ministoci 33.

An sake nada Ministocin tsohuwar gwamnati 11inda aka nada 22 sababbi.

A sabuwar gwamnatin an nada dan gidan tsohon Shugaban Kasar Mahamadou Issoufou mai suna Mahamane Sani a matsayin Ministan Man Fetur da, Makamashi.

A ranar 2 ga Afrilu aka rantsar da Bazoum a matsayin Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar bayan lashe zabe zagaye na 2 da aka yi a ranar 21 ga Fabrairu.

 


News Source:   ()