Firaministan Chadi Pahimi Padacke Albert da Majalisar Mulkin Soji ta kasar ta nada ya kafa sabuwar gwamnati.
Mafi yawan Ministocin da aka nada in banda wasu 'yan adawa kadan sun fito ne daga tsohuwar gwamnatin Idris Deby Itno da aka kashe.
An nada Muhammad Ahmad Alhabo a matsayin Ministan Harkokin Waje, Davud Yaya Brahim Ministan Tsaro, Abdramane Kouallamallah Ministan Sadarwa kuma Kakakin Gwamnati inda aka nasa Janaral Suleyman Abakar Adoum a matsayin Ministan Tsaron Jama'a da Gudun Hijira.
Manyan jagororin 'yan adawa sun bayyana rashin amincewa da sabuwar gwamnatin inda suka ce za ta dora ne daga inda tsohuwar gwamnati ta tsaya.