A Libiya an kafa Kwamitin Zaman Lafiya da Hadin Kan Kasa domin tattara al'umar kasar waje guda.
Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Libiya Muhammad Yunus Al-Manfi ya gudanar da taron manema labarai tare da mataimakansa Musa Al-Kuni da Abdullah Al-Lafi a birnin Tarabulus.
A jawabin da Al-Manfi ya yi a wajen ya shaida cewa, an fara aiwatar da shirin da aka dade ana jira wanda zai hada kan al'umar Libiya waje guda karkashin inuwar zaman lafiya.
Shugaban ya kara da cewa, suna fatan za a gudanar da zabuka a Libiya a ranar 24 ga Disamba.
Ya ce, a ranar 1 ga Afrilu kwararru na Libiya sun gudanar da taro domin kafa Kwamitin Zaman Lafiya da Hadin Kan Kasa.
A ranar 5 ga Fabrairu karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva aka gudanar da Taron Sulhun Siyasa na Libiya inda aka amince da Muhammad Al-Manfi ya Shugabanci Kasar sannan Abdulhamid Al-Dibaybe ya zama Firaministan har nan da 24 ga Disamban 2021 da za a gudanar da zabuka.