Wani tsohon jami’in leken asiri ne ya shigar da kara kan Ramaphosa da aikata laifuka biyo bayan kutsawa cikin gonarsa, yana mai zargin shugaban kasar ya aikata ba daidai ba wajen kokarin boye wasu kudade da aka sace na dala miliyan hudu.
Bayan wani bincike da sashen ‘yan sanda na musamman na Hawks ya gudanar, mai gabatar da kara bai gurfanar da kowa a gaban kotu ba duk da irin fatan samun nasara bisa shedar wanda ya shigar da karar
Sama da bayanai 150 ne aka samu a binciken, kamar yadda kakakin hukumar shigar da kara ta kasar ya shaida wa tashar Newzroom Afrika, yana mai cewar shidar da masu gabatar da karar suke da ita ta sa dole ba za a iya ci gaba da shari’ar ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI