An jibge sojoji a Dakar Babban Birnin Sanagal

An jibge sojoji a Dakar Babban Birnin Sanagal

Sakamakon zanga-zangar da aka fara a kasar Sanagal bayan kama madugun 'yan adawa kuma shugaban jam'iyar PASTEF Ousmane Sonko, an jibge sojoji a Dakar Babban Birnin Kasar.

Bayan da 'yan adawa da kungiyoyin farar hula suka yi kira a karshen mako da a fara zanga-zanga ta tsawon kwanaki 3 a fadin Sanagal, gwamnatin kasar ta fara jibge sojoji a Dakar da kewayen birnin.

An tsaurara matakan tsaro sakamakon hasashen zanga-zangar za ta yi tsamari a wannan makon.

Duk da an janye tuhumar tayar da zaune tsaye da ake yi wa Sonko da kuma sakin sa da aka yi, amma ana fargabar za a ci gaba da zanga-zangar a Sanagal.

Shafin Twitter na ofishin jakadancin Turkiyya a Dakar ya gargadi 'yan kasar da kar su fita waje a wannan lokaci matukar ba ta kama dole ba.

Sakamakon haka an dakatar da aiyuka a ofishin jakadancin a ranar Litinin din nan.

A gefe guda, mutane miliyan 1,3 ne suka yada gangamin #freesenegal da ake yi tsawon kwanaki 3.

'Yan wasa, mawaka, 'yan kwallon kafa da sanannun mutane 'yan Afirka sun dinga yada gangamin a shafukan sada zumunta.

A daidai lokacin da hakan ke faruwa, tsohon Shugaban Kasar Sanagal Abdullahi Wade ya yi kira ga Shugaba mai cinMacky Salla da kar ya saurari Ministan Harkokin Cikin Gida Antoine Felix Diome.


News Source:   ()