An jibge dakarun Tarayyar Habasha da dama a jihar Amhara

An jibge dakarun Tarayyar Habasha da dama a jihar Amhara

Kungiyar Fano, mashahuran tsagerun  na kabilar Amhara, na biyu a Habasha, sun dauki makamai a kan gwamnatin Habasha a watan Afrilun 2023 a wannan yanki mai mutane miliyan 23.

Wani yankin da yaki ya tilastawa mutane tserewa a Habasha Wani yankin da yaki ya tilastawa mutane tserewa a Habasha © Sébastien Németh / RFI

Rikicin dai ya samo asali ne sakamakon muradin gwamnatin tarayya na kwance damarar jami’an tsaron yankin Fano da na Amhara.

Wasu daga cikin mazauna yankin Amhara Wasu daga cikin mazauna yankin Amhara AFP - EDUARDO SOTERAS

A watan Agustan 2023, gwamnati ta ayyana dokar ta baci a Amhara, wadda ta kare a watan Yuni. "A cikin makonni biyu da suka gabata, an aika da sojoji da yawa  da kuma kama wasu ma'aikatan gwamnati da ake zargi da hada baki da kungiyar ta Fano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)