Ƴan jarida sun tsunduma yajin aiki a Senegal

Ƴan jarida sun tsunduma yajin aiki a Senegal

Shugaban Ƙungiyar Mawallafa Labarai ta Senegal, Mamadou Ibra Kane ya bayyana cewa, daga wannan Talatar, za a katse tashoshin rediyo da talabijin da shafukan labarai na intanet .

Da ma dai ɓangaren jarida a Senegal ya jima yana fuskantar matsalar tattalin arziƙi, sannan da dama daga cikin wakilan da ke bada rahotanni sun sha ƙorafi kan rashin kyawun yanayin aiki.

Sai dai a baya-bayan, ɓangaren na aikin jarida ya daɗa fuskantar barazana sakamakon kalaman firaministan ƙasar Ousmane Sonko da ƴan jarida ke kallo a matsayin barazana ga aikinsu.

Sonko wanda ya ɗare kan muƙaminsa a cikin watan Afrilun da ya gabata, ya caccaki kafafen yaɗa labaran da ya ce, suna wallafa duk abin da suka ga dama ba tare da dogara da kwararan majiyoyi ba da sunan ƴanci.

Kazalika ya yi tur da abin da ya kira ‘ɓarnatar da dukiyar talakawa’ da ake yi a ɓangaren aikin jarida, yana mai zargin shugabannin kafafen yaɗa labaran da rashin biyan kuɗin samar da tsaro ga al’ummar ƙasar.

Sai dai a martanin da kungiyar ma’aikatan jaridar ta mayar, ta bayyana matakin na Sonko a matsayin yunƙurin daƙile yaɗa labarai tare da musguna wa ƴan jaridar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)