An ja tunga tsakanin masu haƙar ma'adanai da mahukuntan Afrika ta kudu

An ja tunga tsakanin masu haƙar ma'adanai da mahukuntan Afrika ta kudu

Jami’an sun kuma iya nasarar ceto wasu da ransu, wanda adadinsu ya kai 166 ko da ya ke tuni aka tisa ƙeyarsu don fuskanta hukunci kan abin da gwamnatin ƙasar ta kira zagon ƙasa da karya dokokin haramcin haƙar ma’adinai a mahaƙun waɗanda aka dakatar da aiki a cikinsu tsawon shekaru.

Gwamnatin Afrika ta kudu ta ce kaso mai yawa na waɗannan masu haramtaccen aikin haƙar ma’adinai ba ƴan ƙasar ba ne, ƴan cirani ne da suka shigo daga ƙetare.

Tun cikin watan Agustan bara ne gwamnatin Afrika ta kudu ta sanya jami’ai su yiwa dukkanin haramtattun mahaƙun ƙawanya, wanda ya kange damar iya isar musu da abinci ko da ya ke suma sunja tunga ta yadda suka ƙi yadda da fitowa daga ramukan.

Wannan mataki na gwamnati ya sanya tarin mahaƙun rasa rayukansu saboda yunwa da kuma ƙishirwa batun da ya janyowa ƙasar kakkausar suka daga ƙasashe da ƙungiyoyin kare haƙƙin dan adam.

Kakakin rundunar ƴan sandan Afrika ta kudu Athlenda Mathe ya ce suna ci gaba da matsa ƙaimi don ganin masu haƙar ma’adinan sun miƙa wuya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)