Jagoran wanda ya gina wani masallaci da niyya mayar da shi mafaka ga masu ra’ayin auren jinsi musulmai a kasar , yana cikin wata mota ne tare da wani mutum a lokacin da wata mota ta tsaya a gabansu ta tare hanyar, in ji 'yan sanda.
“Wasu mutane biyu da ba a san ko su waye ba da fuskokinsu a rufe sun fito daga cikin motar inda suka fara harbi kan motar,” a cewar rundunar ‘yan sandan ta Eastern Cape a cikin wata sanarwa.
"Daga nan sai suka gudu daga wurin, kuma direban ya lura cewa an harbe Hendricks, wanda ke zaune a bayan motar kuma an kashe shi." Wata mai magana da yawun ‘yan sanda ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP sahihancin wani faifan bidiyo da aka nuna a shafukan sada zumunta wanda ke nuni da wani kisan gilla a Bethelsdorp da ke kusa da Gqeberha, wadda a da ake kira Port Elizabeth.
“Ba a san dalilin kisan ba, kuma wani bangare ne na binciken da ake yi,” in ji ‘yan sanda, tare da yin kira ga duk wanda ke da bayanai da ya fito. Kungiyar masu auren jinsi ta duniya, ta yi tir da kisan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI