An haramta bikin tunawa da kifar da gwamnatin Blaise Compaore a Burkina Faso

An haramta bikin tunawa da kifar da gwamnatin Blaise Compaore a Burkina Faso

Wasu fusatattun matasa da kuma 'yan siyasa ne suka kaddamar da zanga zanga a ranar 21 ga watan Oktobar shekarar 2014 lokacin da shugaban kasar Burkina Faso Balaise Compaore ya kudiri aniyar amfani da majalisar dokokin kasa domin sauya kundin tsarin mulkin kasar da zai ba shi damar ci gaba da zama a karagar mulki.

Zanga zangar ta fara kazanta daga ranar 28 ga wata zuwa 31 ga wata, lokacin da matasan suka kutsa kai majalisar dokoki suka kuma banka mata wuta domin nuna fushinsu.

Wannan ba shi ne karo na farko da shugaban ke sauya kundin tsarin mulki ba, amma a wannan karon jama'ar kasar suka nuna masa cewar ba za su iya hakuri ba, saboda haka suka kaddamar da zanga zanga domin ganin majalisar dokokin kasar wadda jam'iyarsa ke da kashi biyu bisa 3 na 'yan majalisu ba ta biyawa shugaban bukatarsa ba.

Wadanda suka shirya zanga zangar sun hada da wasu 'yayan jam'iyar Compaore da suka bijire mata suka kuma kafa kawancen 'yan adawa mai suna MPP irin su Roch Christain Marc Kabore, tsohon shugaban majalisar dokoki da Simon Compaore, magajin garin Ouagadougou da Salif Diallo, tsohon minista tare kuma ga goyan bayan kungiyoyin kwadagon kasar.

Wannan zanga zangar ta tilastawa Compaore tserewa ya bar Burkian Faso, abinda ya kawo karshen mulkinsa na shekaru 27 bayan juyin mulkin da ya yi wajen hallaka abokinsa kuma fitaccen shugaban kasa Thomas Sankara da ya yi farin jini a Afirka a kan manufofinsa na ci gaban nahiyar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)