Kwamitin shugaban kasar Libiya ta sanar da cewa an haramta duk wasu ayyukan soji a kasar ba tare da amincewar kwamitin zartarwar kasar ba.
A cikin bayanin da aka yada a shafin Twitter na sashen watsa labaran Faramakin Fushin Volcano an bayyana matakan da aka dauka akan lamurran soja a kasar.
A cikin takaddar, an sanar da haramta da dakatar da zirga-zirgan sojoji, sauya gurin aiki da kuma sauyawa makamai wuraren da suke ba tare da izini ba.
A takardar da aka wallafa an bayyana cewa "an ba da umarnin aiwatar da umarnin nan take a dukkan rundunonin soja dake fadin kasar."
Bugu da kari, an kara jaddada matakin a sanarwar, inda aka bayyana cewa "Bayan da mayakan sa kai masu biyayya ga mai aikata laifukan yaki Haftar suka dauki mataki a cikin ayarin motocin a kuduncin kasar, an haramta duk wani farmaki ba tare da amincewar majalisar shugaban kasar Libiya ba."
An bayar da rahoton cewa sojojin sa-kai masu biyayya ga soja Khalifa Haftar, shugaban masu dauke da makamai a gabashin Libiya, sun ayyana yankin a matsayin wani yankin sojoji da aka hana sojoji kai farmaki a yankin inda suka hana kai-kawo kan iyakar kasar da Aljeriya.
Shafin yanar gizo mai zaman kansa a Libiya, "Ean Libya", ya ruwaito cewa mayakan sa kai na Haftar sun karbe iko da kofar iyakar Iseyyin tsakanin Algeria da Libiya a kuduncin kasar.
Mayakan na Haftar sun sanar a ranar 17 ga watan Yuni cewa sun fara wani atasayen soji a kudancin kasar.