An haramta aiyukan wata kungiyar farar hula ta Faransa a Nijar

An haramta aiyukan wata kungiyar farar hula ta Faransa a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, an haramtawa kungiyar farar hula ta Faransa (Acted) gudanar da aiyuka sakamakon zargin ta da alaka da wata kungiyar ta'adda.

Gwamnan yankin Diffa Issa Lemine ya shaida cewa, har na da lokacin da za a fitar da sanarwa ta gaba, an haramta aiyukan Acted a Diffa kuma tuni aka fara gudanar da bincike game da kungiyar.

Lemine ya kara da cewa, ba a amince da yadda kungiyar ke gudanar da aiyukanta ba, kuma sun sami labarin ma tana da alaka da wata kungiyar ta'adda, hakan ya sanya suka dauki mataki har zuwa lokacin da za a tabbatar da gasjiyar zargin da ake yi.

Sanarwar ba ta bayyana wacce kungiyar ta'adda ce ke da alaka da Acted ba.

Tun shekarar 2010 Acted ta ke gudanar da aiyukan jin kai ga wadanda rikici ya raba da matsugunansu a Jamhuriyar Nijar.


News Source:   ()