An hana jami'an hambararriyar gwamnatin Gini fita kasashen waje

An hana jami'an hambararriyar gwamnatin Gini fita kasashen waje

Sojojin da suka kifar da zababbiyar gwamnatin farar hula a Gini sun hana hambararren Shugaban Kasar Alpha Conde da sauran mukarraban gwamnatinsa fita daga kasar.

Labaran da jaridun Gini suka fitar sun bayyana cewa, jagoran juyin mulkin Laftanal Kanal Mamady Doumbouya ya gana da jami'an gwamnati da sauran manyan ma'aikata a fadar Sekoutoreye.

Doumbouya ya shaida cewa, 'yan bokon kasar Gini sun dandanawa mutanen kasar kuda tare da wanzar da rashin adalci, kuma domin hana kasar yin alkafira, a matsayinsu na Kwamitin Hadin Kan Kasa da Cigaba sun karbe mulki.

Ya zayyana cewa, za su samar da yanayin da za a kafa sabuwar gwamnatin da za ta tafi da kowanne bangare na al'umar kasar, kuma ba za su dauki fansa, kyama ko tsanar wasu mutane ba.

Dambouya ya kara da cewa har zuwa lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati babu wani jami'İn tsohuwar gwamnatin da aka fitar da zai fita kasar waje, ya kuma bukaci su mka fasfunansu da motocin da suke hawa na gwamnati.

Jagoran 'yan juyin mulkin ya kuma kara da cewa, suna bayar da muhimmanci ga masu zuba jari na kasashen waje, kuma sun sake bude iyakokin sama na kasar.

A safiyar Lahadin nan ne aka jiyo karar harbe-harbe a yankin da Fadar Shugaban Kasar Gini Sekotoureye take da ke Conakry Babban Birnin Kasar.

Bayan awanni da afkuwar lamarin, Shugaban Dakaru na Musamman Kanal Mamady Doumbouya ya sanar da sun kifar da gwamnati, sannan ya sake fitar da bidiyon da ke nuna sun kama Shugaba Alpha Conde.


News Source:   ()