
Ƴan Tawayen na M23 na ci gaba da samun nasara kan dakarun Sojin Congo da tuni suka ƙwace manyan birane kamar su Goma da Bukavu, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali da fargaba.
Dama dai tuni hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta yi hasashen cewar faɗan na iya tilasatawa mutane gudun hijra zuwa Burundi, wanda dangane da hakan ta fara shirin tallafawa mutane dubu 58, cikin watanni 3, a cewar Brigitte Mukanga-Eno mai magana yawun hukumar a Burundi.
Hukumar ta ce cikin ƙasa da makonni 2, sun karɓi mutane dubu 42 masu neman mafaka sannan dubu 36 sun tsallaka kogin Rusizi kusa da garin Rugombo ,yayin da dubu 6 suka isa wata matattarar ‘yan gudun hijra da ke kusa da babban birnin ƙasar,Bujumbura.
Ko a makon da ya gabata, sai da mutane sama da dubu 9 suka shiga ƙasar a rana guda ,a wani yanayi da hukumar ke neman aƙalla dala miliyan 40 da dubu 400 domin taimakawa ‘yan gudun hijira dubu 275 daga kudanci da Arewacin Kivu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI