
'Yan adawa da kungiyoyin farar hula a ƙasar ta Togo na kallon hakan a matsayin hanyar da shugaban kasa mai ci Faure Gnassingbe zai ci gaba da mulki har abada, yayin da tsohon kundin tsarin mulkin kasar ya bashi damar tsayawa takara a wa'adi na karshe a wannan shekara ta 2025.
"Tsarin mulki ne wanda ba mu taɓa samunsa ba. Dole ne mu fuskanci wannan tsari da ya dace abokanin siyasa su cimma fahimtar juna kuma mu yaba da shi," Vimenyo Koffi, wani dan majalisar karamar hukumar da ya kada kuri'a da sanyin safiyar Asabar a Lomé, ya shaida wa AFP.
Kansilolin ƙananan hukumomi 1,527 da kuma kansiloli 179 ne aka kira domin kada ƙuri’ar zaɓen ‘yan majalisar dattawa 41 da za su zauna a sabuwar majalisar dattawa da aka samar. 'Yan takara 89 ne suka fafata.
Majalisar dattijai zata kunshi mambobi 61 gaba ɗaya, 20 daga cikinsu ne shugaban majalisar ministocin zai nada su.
Tare da sabon kundin tsarin mulki, ofishin shugaban kasar zai kasance na girmamawa ne kawai kuma zai tabbatar da gudanar da mulki mai inganci daga shugaban majalisar wanda dole ne ya kasance shugaban jam'iyya mai rinjaye a majalisar dokokin kasar.
A wannan yanayin, Faure Gnassingbe ne, ke kan karagar mulki tun shekara ta 2005 bayan mahaifinsa wanda ya ci gaba da shugabancin kasar kusan shekaru 38.
Jam'iyyarsa ta Union for the Republic (Unir), ta lashe zaɓen 'yan majalisar dokoki na watan Afrilu da gagarumin rinjaye, inda ta samu kujeru 108 cikin 113.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI