An gudanar da Taron Kwamitin Sulhun Kasa na Libiya a Tarabulus

An gudanar da Taron Kwamitin Sulhun Kasa na Libiya a Tarabulus

A Tarabulus Babban Birnin Libiya an gudanar da Taron Kwamitin Sulhun Kasa wanda zai assasa tushen zaman lafiyar jama'ar kasar.

Rubutacciyar Sanarwar da aka fitar daga Majalisar Shugabancin Libiya ta bayyana cewa, daga cikin wadanda suka halarci Taron Kwamitin Sulhun Kasa na Libiya akwai Mataimakan Shugaban Majalisar Shugabanci ta Libiya Abdullah Al-Lafi da Al-Kuni, Ministar Shari'a Halima Ibrahim da Ministan Wadanda Aka Raba da Matsugunansu Ahmad Abu Huzam.

Haka zalika Wakilin Shirin Cigaba na Majalisar Dinkin Duniya a Libiya Gerardo Noto, Jami'in Aiyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya a Libiya Georgette Gagnon da Wakiliyar Libiya a Tarayyar Afirka Wahida Al-Ayari ma sun halarci Taron ta yanar gizo.

A jawabin da Al-Lafi ya yi a wajen Taron ya yi nuni ga muhimmancin da Zulhun Kasa yake da shi wajen assasa zaman lafiya da gudanar da zabe a Libiya.

Abu Huzam kuma ya bayyana cewa, ta hanyar taimakon da gwamnati ke baiwa Kwamitin, wadanda suka yi gudun hijira a ciki da wajen Libiya za su samu damar komawa yankunansu.

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya Gagnon kuma ya sake jaddada goyon bayan Majalisar ga duk wani shiri da zai kawo zaman lafiya a Libiya.

Wakilin UNDP a Libiya Noto kuma ya taya Libiya murna bisa samar da wannan Kwamiti da kuma irin aiyukan da yake gudanarwa.

A ranar 6 ga Afrilu ne Majalisar Gudanarwa ta Libiya ta Sanar da Kafa Kwamitin Sulhun Kasa.

Ana sa ran Kwamitin zai ci gaba da gudanar da taro har nan da wata daya.

 


News Source:   ()