An gano yadda aka yiwa daruruwan mutane allurar riga-kafin Corona jabu a Yuganda

An gano yadda aka yiwa daruruwan mutane allurar riga-kafin Corona jabu a Yuganda

A kasar Yuganda an yi wa a kalla mutane 800 allurar riga-kafin Corona ta jabu.

An bayyana cewa, an yi allurar riga-kafin ta jabu a asibitoci masu zaman kansu da ke kewayen Kampala Babban Birnin Yuganda.

Jami'İn lafiya Warren Namara ya fitar da sanarwa game da batun inda ya ce,

"Daga tsakiyar watan Mayu uwa karshen Yuni an yi wa a kalla mutane 800 allurar riga-kafin ta jabu a Yuganda.  Wata kila an bawa mutane da dama wannan abu."

An kama mutane 2 tare da wani likita game da almundahanar.

Alkaluman Ma'aikatar Lafiya ta Yuganda sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu an mutane sama da dubu 79 cutar Corona a kasar, kuma kusan mutane 900 annobar ta yi ajali. An kuma yi alluran riga-kafi dubu 843.

 


News Source:   ()