An gano wani babban kabari a gabashin Ruwanda wanda aka kiyasta an binne kusan mutane 5,000 da aka kashe a kisan kisan kare dangi a ciki.
Wani jami’in yankin, Richard Gasana ya fadawa manema labarai cewa an gano kabarin a yankin Gatsibo na kasar, inda aka yi kisa gilla bisa umarnin tsohon Gwamnan Murambi, Jean Baptiste Gatete.
Gasana ya bayyana cewar kaburburan wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda aka fitar bayan sun samu mafaka a cocin Katolika na Kiziguro yayin kisan kare dangin suna da zurfin mita 30 kuma ana tsamanin aikin hakar za ta dauki makonni 3.
Kotun hukunta manyan laifuka ta Ruwanda ta gurfanar da Gatete wanda ya yi aiki a matsayin gwamnan gundumar Murambi daga shekarar 1987 zuwa 1993 sannan daga baya ya ci gaba da siyasarsa a yankin kuma aka yanke masa hukuncin shekaru 40 a kurkuku.
Dangane da alkaluman hukuma, an gano ragowar kusan mutane 118,000 da aka yiwa kisan kare dangi a kasar daga shekarar 2018 zuwa 2019.
A Ruwanda a shekarar 1994, ‘yan Hutu suka kaddamar da kisan kare dangi kan 'yan Tutsi, wanda suka dauki alhakin hatsarin jirgin saman Shugaba Juvenal Habyarimana na wancan lokacin.
An kashe ‘yan Tutsi sama da dubu 800 a kisan kare dangin a cikin kwanaki 100 a kasar.