An sake gano jikkunan mutane 7 a garin Terhune na kasar Libiya, wanda dakarun kasar suka kubutara ranar 5 ga Yuni.
Shugaba Hukumar Neman Mutanen da Suka Bata ta Libiya Kamal Al-Sayawi ya shaidawa manema labarai cewar a aiyukan neman mutane da ake yi a Terhune an sake gano gawarwakin mutane 7.
Sayawi ya fadi cewar an aike da gawarwakin zuwa asibiti don a tabbatar da meye ya yi ajalinsu.
Bayan kubutar da garin Terhune wanda dan tawaye Haftar yake amfani da shi tsawon watanni 14 a matsayin cibiyar diban mai don kai hare-hare a Tarabulus, jami'an gwamnatin Libiya suka bayyana akwai kaburbura 11 da aka binne mutane da yawa a cikinsu a yankin.
A ranar 22 ga watan Yuni Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta fitar da sanarwar cewa sun samu kwararan bayanai da ke tabbatar da an samu kaburbura 11 da aka binne mutane da dama a cikinsu a yankin Terhune.