An gano jirage dauke da sojojin haya daga Siriya zuwa Libiya

An gano jirage dauke da sojojin haya daga Siriya zuwa Libiya

Bayan tsagaita wutar da aka kaddamar a watan Oktoba, an gano jiragen sama 74 a Libiya dauke da sojojin haya daga Siriya zuwa yankunan da ke karkashin ikon Khalifa Haftar, shugaban sojojin ‘yan tawaye a gabashin kasar.

A cewar wata sanarwa da sojojin Libiya suka fitar, jiragen da suka tashi daga babban birnin Damascus da kuma daga sansanin Humeymim da ke karkashin ikon Rasha a Latakia sun sauka a filin tashi da saukar jirage na Benina da ke Benghazi.

Jiragen na Kamfanin Cham Wings, na dangin Bashar Assad, su ma suna sauka a sansanin soja na Al-Hadim da ke karkashin Daular Larabawa.

Jiragen na shiga sararin samaniyar Libiya a boye.

A karkashin Farmakin Volcano of Rage, wanda ke da alaka da sojojin Libiya, an jaddada cewa jiragen sun sabawa dokokin Majalisar Dinkin Duniya da kuma yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanya wa hannu a shekarar 2020. 


News Source:   ()