A yankin Benghazi da ke hannun dan tawaye Haftar na Libiya an gano jikkunan mutane 11.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, an gano jikkunan mutanen a kusa da wani kamfanin siminti da ke yankin Al-Hawari na Benghazi.
Majiyoyin sun bayyana cewa, an ga alamun harbi a jiki da fuskokin mutanen, kuma ana tunani an dauki kwanaki 10 da kashe su.
Masu kare hakkokin dan adam na cewa, mayakan Haftar na yawan take hakkokin dan adam a Benghazi.
Shugabannin kabilun Libiya da ke goyawa Haftar baya sun fitar da sanarwa a ranar 15 ga Maris inda suka yi kira da a fitar da mayakan Haftar daga Benghazi.