An gano jami'ar Oxford za ta gwada maganin Corona a Afirka

An gano jami'ar Oxford za ta gwada maganin Corona a Afirka

An gano cewar ana shirin gwada maganin da jami'ar Oxford ta samar don yaki da cutar Corona a kasar Kenya da ke nahiyar Afirka.

Bayanan aiyukan kula da lafiya da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar sun bayyana za a gwada maganin a kan 'yan sama da shekaru 18 su 400 don ganin ko maganin zai hana su kamuwa da cutar kuwa a'a.

Aikin gwajin zai dauki tsawon shekaru 2 wanda Cibiyar Bincike Kan Samar da Magunguna ta Kenya (KEMRI) za ta yi tare da Cibiyar Bincike ta Welcome Trust.

Lamarin ya ja hankali kan yadda likitoci, masu samar da magunguna da ma'aikatan jiyya ne kawai za su yi aikin inda 'yan sa kai za su bayar da kawunansu don yin gwajin.

Sannan an bayyana cewar za a zabi wadanda suka amince a yi gwajin a kansu a garuruwan Kilifi da Mombasa da cutar ta yadu sosai.

A watan da ya gabata Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ba za a yi amfani da 'yan kasarsa ba wajen gwajin maganin na Corona ba.

Har yanzu ba a gama tabbatar da ko gwamnatin ta Kenya ta amince a yi gwajin ba.


News Source:   www.trt.net.tr