An gano gwarwaki 30 cikin wani kwale-kwale a gaɓar tekun Senegal

An gano gwarwaki 30 cikin wani kwale-kwale a gaɓar tekun Senegal

Sanarwar da kakakin rundunar sojin Senegal, Ibrahima Sow ya fitar ta ce an sanar da sojojin ruwa halin da jirgin ke ciki a  yammacin Lahadin da ta gabata, wanda ba tare da bata lokaci ba suka aike da  tawagar sintiri zuwa yankin mai tazarar kilomita 70 daga Dakar.

A cewar rundunar sojin, tana ci gaba da  bincike domin tabbatar da adadin mutanen da suka mutu da kuma yankunan da suka futo.

Ko a  farkon watan nan na Satumba,  sai da wani jirgin ruwa dauke da mutane 89 ya kife a gabar tekun kasar Senegal, wanda  akalla mutane 37 ne suka mutu, a cewar hukumomin Senegal.

Yawancin baƙin hauren da ke barin Afirka ta Yamma ta kasar Senegal su na tsere wa tashe-tashen hankula ne da  talauci da rashin aikin yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)