A cikin kwanaki 40 da suka gabata, an gano gawarwakin mutane 225 da aka binne a ramuka guda a yankin Terhune da ke kudancin Tarabulus Babban Birnin Libiya.
Sanarwar da aka fitar daga ofishin Farmakan Fushin Dutse Mai Aman Wuta da Dakarun Libiya ke kaiwa ta ce, a cikin kwanaki 40 an gano gawarwaki 225 a yankunan da aka kwace daga hannun mayaka mabiya dan tawaye Haftar Khalifa da ke kudancin kasar.
Sanarwar ta ce tun bayan kwace Terhune daga hannun 'yan tawayen aka fara gudanar da aiyukan bincike da neman jikkunan mutanen da aka kashe tare da binnewa a ramuka guda.