A yankin Timbuktu na kasar Mali, an gano gawar wani Shugaban wata gunduma da aka yi garkuwa da shi.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce a ranar 13 ga Yuli ne wasu da ba a san ko su waye ba suka yi garkuwa da shugaban gundumar Garba-Koira mai suna Abdoulaye Alpha.
Ana zargin an kashe Alpha ne sakamakon rikicin da yake yi da abokan adawarsa na siyasa a kasar.