An gabatar da kudirin tsige mataimakin shugaban kasar Kenya Gachagua

An gabatar da kudirin tsige mataimakin shugaban kasar Kenya Gachagua

Shugaban majalisar dokokin kasar Moses Wetang'ula ya ce sama da kashi daya bisa 3 na 'yan majalisun dokokin kasar suka rattaba hannu a bukatar tsige mataimakin shugaban kasar wanda 'dan majalisa Mwengi Mutuse, wani na kusa da shugaban kasa Ruto ya gabatar.

Daga cikin korafin da ake yi a kan mataimakin shugaban kasar Gachagua harda hana bai wa jama'ar kasa damar samun gurabun ayyukan gwamnati da kuma raba dukiyar kasa tare da goyan bayan zanga zangar adawa da gwamnati.

Takaddama tsakanin shugaba Ruto da mataimakinsa Gachagua ta fito fili a 'yan kwanakin nan, abinda ya sa mataimakin bayyana bacin ransa dangane da abinda ya kira mayar da shi saniyar ware wajen gudanar da mulki, ya yin da ya nesanta kansa da magoya bayan sa daga zanga zangar adawa da gwamnatin da akayi a farkon wannan shekarar.

Wannan shi ne karo na farko da za'a gwada amfani da kundin tsarin mulkin da aka rubuta a shekarar 2010 wajen tsige mataimakin shugaban kasa daga ofishinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)