An ga motsin mayakan Haftar a kudancin Libiya

An ga motsin mayakan Haftar a kudancin Libiya

Rundunar sojin Libiya ta bayyana cewa, an ga motsin ayarin motocin mayakan dan tawaye Haftar dauke da manyan makamai a yankin Shuwarif da ke kudu maso-gabashin Tarabulus Babban Birnin kasar.

Sanarwar da aka fitar daga ofishin Farmakan Fushin Dutse Mai Aman Wuta ta ce, "An ga mayakan Haftar dan tawaye mai aikata muggan laifuka tare da taimakon Rasha dauke da manyan makamai sun gifta ta yankin Shuwarif."

Sanarwar ta ce, a jerin gwanon motocin mayakan akwai motocin yaki 63, tirelolin daukar jigida 3 da garkuwar makamai masu linzami kirar Rasha ta Pantsir S1 da ke kan wata mota kirar Jamus.

Sanarwar ta kuma ce, wannan motsi da makamai da mayakan Haftar ke yi ya karya yarjejeniyar 5+5 ta soji da aka sanya hannu a kai a tsakanin 19-23 ga watan Oktoban 2020 a garin Geneva na kasar Swizalan.

 


News Source:   ()