Kungiyar wadanda aka azabtar da su a Togo (ASVITTO), wadda ita ma manufarta ita ce sanya ido kan wuraren da aka hana ‘yancin walwala, ta koka matuka tare da yin kira ga hukumomin wannan kasa na ganin su dauki matakai da suka dace.
Birnin Lome Photothek via Getty Images - Ute GrabowskyRahotanni daga kasar na nuni cewa an dau kusan tsawon sa'o'i uku a ranar Litinin da sa'o'i shida a ranar Talata, gidan yarin Lomé ya kasance babu wutar lantarki.A wadana ranaku,fursunoni a gidan yarin na Lome sun fuskanci matsi da zafi fiye da yada ake zato,duk da cewa hukumomin kasar ba su dau matakan da suka dace a kai ba.
Kasuwar birnin Lome © AFPYayin tattaunawa da Magali Lagrange , shugaban kungiyar ASVITTO Acholi Kao, ya jaddada cewa gidan yarin na Lomé da aka gina da nufin ya dauki fursunoni 600, a halin yanzu yana dauke da kusan fursunoni 2,000".
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI