Rahotanni daga kasar na nuni cewa ruwan sama mai karfi a farkon damina ya sauka a Kinshasa, babban birni mai kusan mutane miliyan 17, bisa ga shaidu da hotuna da aka buga a shafukan sada zumunta.
A cikin aƙalla bidiyo biyu, an ga motocin bas ɗin jigilar jama'a da ruwa suka tafi da su a tsakiyar titi. A tsakiyar babban birnin kasar, kananan koguna,da magudanan ruwa sun cika, musamman a gundumar masana'antu ta Limete. A matakin "Première Rue", mazauna da suka kuskura su fita da ƙafa sun sami kansu da ruwa har zuwa ƙirjinsu, a cewar shaidu.
Birnin Kinshasa AP - Mosa'ab Elshamy
"Wannan ba shi ne karon farko da muka ga ambaliyar ruwa a nan ba, a duk lokacin da aka yi ruwan sama muna fama da su, saboda rashin tsaftace kogin Kalamu," wani mutum mai shekaru arba'in,yayin da ya kwashe ruwa daga filin da ya mamaye.
Wajen tsallaka ruwan laka, mazauna yankunan Forgeron da Funa, sun samu tallafin matasa don jigilar su a bayansu ko a cikin keken hannu, kan kuɗi kaɗan.
Ambaliya a Africa © AP
Yayin da sararin samaniyar ke muma alamatr wani sabon hadarin inda mazaunan unguwani ke bayyana fargabar na ganin an "ci gaba da samun ruwan sama" saboda rashin tsaftace magudanan ruwa da koguna na babban birnin kasar.
A Kinshasa, ruwan sama da ambaliya a kai a kai na lakume wadanda abin ya shafa. A watan Nuwamban shekarar 2019, kusan mutane arba'in ne suka mutu a babban birnin kasar, sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI