An fitar da sakamakon karshe a hukumance na zaben Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar inda aka tabbatar da samun nasarar Mohamed Bazoum.
Sanarwar da Kotun Koli ta fitar ta ce, Bazoum ya samu kaso 55,66 na kuri'un da aka jefa, inda abokin takararsa Mahame Ousmane ya samu kaso 44,34 a zagaye na 2 na zaben da aka gudanar.
A ranar 2 ga Afrilu za a rantsar da Bazoum a matsayin sabon Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar.
A ranar 27 ga Disamban 2020 aka gudanar da zagayen farko na zabe a Nijar, a ranar 21 ga Fabrairu kuma aka gudanar da zagaye na biyu na zaben.
A ranar 23 ga Fabrairu Hukumar Zabe ta Kasa ta Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa, dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya Bazoum ya samu kaso 55,75 na kuri'un da aka jefa wanda hakan ya ba shi nasarar zama Shugaban Kasa.
An bayyana cewa, dan takarar jam'iyyar adawa ta RDE-Tchanji kuma tsohon Shugaban Kasar Ousmane mai shekaru 71 ya samu kaso 44,25.
Shugaban Kasar Nijar na yanzu Mohammadou Issoufou bai iya sake tsayawa takara ba saboda kammala wa'adinsa na zango 2 da ya yi.