An fitar da jadawalin gasar cin kofin kasashen Afrika na ƴan wasan da ke taka leda a gida

An fitar da jadawalin gasar cin kofin kasashen Afrika na ƴan wasan da ke taka leda a gida

An sanar da jadawalin ne yayin wani bikin da aka gudanar ranar Laraba a Kenyatta International Convention Centre dake birnin Nairobi a ƙasar Kenya.

Kenya mai masaukin baƙi tana rukunin A da ya haɗa da Morocco da Jamhuriyar Demokradiyar Congo da Angola da kuma Zambia.

Tanzania, wadda za ta shirya wasu daga cikin wasannin tana rukuni na B da ya haɗa da Madagascar da Mauritania da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Uganda wadda ke cikin masu haɗakar shirya gasar CHAN tana rukuni na C da ya ƙunshi Niger da Guinea da wasu kasashe biyu da za a bayyana nan gaba.

Mai rike da kofin CHAN Senegal tana rukuni na D da ya shafi Congo da Sudan da kuma Najeriya.

Daga baya za a samu tawaga biyu da za su cike gurbin da ya rage tsakanin Algeria da Comoros da Gambia da Malawi da Masar da Afrika ta Kudu da kuma Gabon.

An ƙirkiro gasarne domin bai wa ƴan wasan da ke taka leda a gida su nuna bajintarsu a wasannin CHAN.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)