An fara yiwa al'umman kasar Libiya allurar riga-kafin kwayar cutar Korona

An fara yiwa al'umman kasar Libiya allurar riga-kafin kwayar cutar Korona

Firaiministan Gwamnatin Hadin Gwiwa ta Libiya Abdulhamid Dibeybe a taron manema labaran da ya gudanar a Tripoli babban birnin kasar ya shadawa manema labarai cewa an fara yiwa dibbin al'umman kasar allurar rigakafin Korona.

Dibeyde da yake bayyana cewa safaran alluran rigakafi zuwa kasar bai zo da sauki ba ya kara da cewa ya tattauna da shugabanin da dama akan hakan inda ya kara da cewa an yi sanarar samar da allurar ga kasar kuma shi da iyalansa ma anyi musu na farko.

Shugaban yaki da yaduwar cututtuka ta kasar Bedreddin en-Neccar ya bayyana cewa za'a fara yiwa ma'aikatan lafiya, tsofaffi da wadanda ke da miyagun cututtuka allurar riga-kafin daga bisani kuam sai ayi wa sauaran al'umma.

 


News Source:   ()