A karon farko an yi magana da 'yan fashin teku da suka yi garkuwa da Turkawa ma'aikatan jirgin ruwan kaya na Mozart mai tutar Laberiya a gabar tekun Najeriya.
'Yan fashin tekun sun kira ofishin kamfanin jirgin ruwan da ke kasar Jamus. Matukin jirgin ya yi magana da mahukuntan kamfanin, kuma ya kira sunayen dukkan ma'aikatan inda ya nuna suna cikin koshin lafiya.
Sanarwar da kamfanin jiragen ruwa na Boden ya fitar ta ce,
"An yi magana da ma'aikatan jirgin ruwa su 15 da aka yi garkuwa da su a kusa da Sao Tome a ranar 23 ga Janairun 2021. Dukkan ma'aikatan su 15 suna cikin koshin lafiya. Babu wanda wani abu ya same shi."
Sanarwar ta ce, babban abun da aka mayar da hankali a kai shi ne a ga an saki mutanen cikin sauri. Kuma ba za a fadi karin wani abu ba game lafiya da tsaron iyalan mutanen.
Jirgin kirar kamfanin Mozart na Ingila, ya fuskanci hari daga 'yan fashin teku a gabar tekun Najeriya a ranar 23 ga janairu.
'Yan fashin tekun sun kashe dan kasar Azabaijan 1, sun yi garkuwa da mutane 15 inda wasu mutanen 3 suka isa tashar jiragen ruwa ta Port-Gentil da ke Gabon da jirgin dakon kayan.